Fassarar Littafin (رسالة إلى السجناء) #WASIKA_ZUWA_GA_YAN_KURKUKU Wallafa - #Abdullah_Jārullah Fassara - #Ibrahim_Al_kisa_i _________________________________ Fitowa ta 0️⃣0️⃣7️⃣(اللسان) Talata,24-10-1441AH/16-06-2020 Abubuwan da ke wajibi ga Wanda ke kurkuku ya Lura dasu 0️⃣6️⃣ - Kuma Kada ya boyu daga tunaninka cewa lalle harcenka makami ne Mai kaifi biyu, ko ka shagaltar dashi a abinda zai anfaneka na zikiri, addu'a da istigfari, ko Shi ya shagaltar dakai da abinda zai cuceka na zagi, tsinuwa, yi da mutane da annamimanci. Wanda dukkanin hakan abubuwa ne na haramci, Kuma masu sabbaba azaba da Shiga wuta kamar yarda Annabi SAW yace: *"Kuma shin akwai abinda ke sabbaba a kifar da mutane a cikin wuta Akan fuskarsu in ba girbe-girben harsunansu ba."* (Tirmizi ya fiddashi, Kuma yace hadisine Mai kyau, ingantarce) Kuma wadannan abubuwan(da aka lissafo na ayyukan harce munana) basa daga siffofin Muminai. ________________________ ✍🏽Ibrahim Al-kisa'i Agege, Lagos Nigeria +2348023225158(WhatsApp) https://facebook.com/ibalkisai #kurkukukuk #sarkar🔥 #addini (في Lagos, Nigeria) https://www.instagram.com/p/CBgd6CBlpIw/?igshid=1r3ku5nqe3k3n










