Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon ma'aikacin VOA, Kabiru Fagge --BBC Hausa
An wallafa a 13:20 16 Disamba 2023 Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar tsohon ma'aikacin gidan radiyon Muryar Amurka, Kabiru Usman Fagge wanda ya rasu ranar Juma'a a Amurka.
Marigayin mai shekara 77 a duniya, ya yi shuhuna tsakanin al'ummar Hausawa a faÉ—in duniya saboda aikin da ya yi da gidan radiyon Muryar Amurka na kimanin shekara 25.
Cikin wata sanarwar saƙon ta'aziyyar da Tinubu ya fitar, ya jinjina wa marigayin saboda ''taimakawar da ya yi wajen gina ƙasa da kuma taimakon da ya bai wa fannin ilimi'', musamman cikin fitaccen shirin da yake gabatarwa na ''Ilimi Garkuwar Dan'adam' a kowanne mako.
"Muna jinjina masa kan yadda ya zaɓi aikin da yake son yi kuma ya haska ƙimar Najeriya a idon duniya," in ji sanarwar.
Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da sauran ɗaukacin al'umar Najeriya da na duniya baki ɗaya.
Source: BBC Hausa











