Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga annabin rahama, annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsa har zuwa tashin qiyama. Bayan haka:
Ya ku bayin Allah. Ubangiji mai girma da buwaya ya horewa bayin hanyoyi daban daban don samin gidan aljannah domin tsananin tausayinsa ga bayinsa.
Allah yana faxa a cikin littafin mai tsarki cewa:
{إِنَّ اللَّهَ اشْتَرَى مِنَ الْمُؤْمِنِينَ أَنْفُسَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ بِأَنَّ لَهُمُ الْجَنَّةَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَيَقْتُلُونَ وَيُقْتَلُونَ وَعْدًا عَلَيْهِ حَقًّا فِي التَّوْرَاةِ وَالْإِنْجِيلِ وَالْقُرْآَنِ وَمَنْ أَوْفَى بِعَهْدِهِ مِنَ اللَّهِ فَاسْتَبْشِرُوا بِبَيْعِكُمُ الَّذِي بَايَعْتُمْ بِهِ وَذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ} [التوبة: 111]
(Lalle Allah ya sayi rayukan muminai da farashin aljanna. Su yi yaqi don xaukaka kalmar Allah, sai su kashe kuma a kashe su. Wannan alkawari ne na gaskiya da ya xaukarwa kansa a cikin Attaurah da Linjila da Alqur'ani. Wanene wanda ya fi Allah cika alkawarinsa?! Don hka ku yi murna da wannan ciniki da kuka yi da Allah. Wannan kuma shi ne babban rabo
An karvo daga Jarir xan Abdullahi ya ce: Mun kasance a wani lokaci a wajen Manzon Allah da daddare, wata yana tsakiyar haskensa, sai Manzon Allah ya ce: “Haqiqa za ku ga Ubangijinku, a fili kamar yadda kuke ganin wannan watan a wannan lokaci, ta bare da turereniya ba. Saboda haka duk kada xayanku ya yarda a fi qarfinsa akan sallar Asuba da ta Magariba". [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Manzon Allah ya ce: “Duk wanda ya yi sallar nafila raka’a goma sha biyu a yini da dare, Allah zai gina masa gida a aljanna. Raka’a biyu kafin asubahi. Raka’a huxu kafin azahar da raka’a biyu a bayanta, da raka’a biyu bayan sallar magariba da raka’a biyu bayan sallar isha’i". Muslim ne ya ruwaito shi.
A game da qiyamullaili, Allah yana cewa;
{تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ يَدْعُونَ رَبَّهُمْ خَوْفًا وَطَمَعًا وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنْفِقُونَ} [السجدة: 16]
(Jukkunansu suna nisa da shimfixinsu. Suna bautawa Ubangijinsu suna masu tsoron azabarsa, masu kwaxayin ladansa. Kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su). Shi ya sa Manzon Allah yake cewa: “Ku yaxa sallama a tsakaninku. ku ciyar da abinci, ku sada zumunci, ku yi sallah da daddare lokacin da mutane suke barci, sai ku shiga aljanna da aminci". [Tirmizi ne ya ruwaito].
www.islamkingdom.com/ha/fagen-imani-wuta-da-aljanna