ZAMAN AURE: MATSALOLIN KAWAYE A CIKIN AURE
Yana daga cikin abin da ke kawo cece-kuce acikin aure da kuma tabarbarewar aure a yau sune kawaye, kamar dai yadda muka sani akwai kawaye na kirki masu san kawarsu da zaman lafiya agidan mijinta , akwai kuma kawayen banza wadanda ba abin da suka aje sai hassada da fitina zasu dinga turawa tsakaninki da mijinki , ko kuma tsakaninki da abokiyar zamanki. Sau dayawa zaka ga mace ta wanke kafarta taje gidan kawarta don kawai ta haddasa fitina. Tana shiga zata fara kintsawa kawar nana mummunan zance, kudin cefane nawa yake baki? Kina adashi? Kina dai tari ko? Daga jin wannan maganganun kasan maganganune wadanda basu da kyau, to daga nan shike nan sai fitina tafara aukuwa acikin gidanka, don haka yar uwa kiji tsoran Allah kini sanci irin wadannan muggan kawaye wadanda basa nufinki da alkhairi sai sharri agidan ki, kuma mazaje kurinka lura da irin wadannan matan wadanda suke kokarin bata maka cikin gidanka. Kullun kana bada tarbiyya amma ana rushe ta, kuma kara ta ina ake rushe ta, to ka bin ciki kawayen ta, Manzon Allah s,a,w yace :idan mace ta sallaci salloli biyar, kuma ta azumci watan ramadan , kuma ta kiyaye farjinta , sannan kuma tabi mijinta, to zata shiga aljannah,; Ahmad bin hambal daga Abi huraira. Wallahu a'alam











